Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

‘Yan sanda sun cafke mai daukar nauyin tsagerun IPOB a jihar Imo

Published

on

‘Yan sandan jihar Imo sun cafke wani mutum da ake zargi da daukar nauyin tsagerun dake fafutukar kafa ‘yantattar kasar Biafra, IPOB.

A wata sanarwa da mai Magana da yawun ‘yan sandan jihar, CSP Mike Abattam ya fitar, ya ce, ana zargin Boniface Okeke da bawa kungiyar tsagerun tallafin naira miliyan 10.

CSP Abattam ya ce, “Okeke ya tabbatar da cewa shi ne mai ba da taimako da kuma kuɗade na ayyukan IPOB a cikin jihar yayin da yake a kasar waje.”

Ya kuma ce, Okeke mai shekaru 57 ya taimakawa ‘yan sanda wajen kama mutane 26 daga cikin mambobin kungiyar tsagerun.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!