Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Manyan kotunan jihar Kano za su fara hutun su na shekara-shekara

Published

on

Manyan kotunan jihar Kano za su fara hutun su na shekara-shekara.

Mai magana da yawun kotun Kano Baba Jbo Ibrahim ne ya bayyana hakan, ta cikin wani saƙon murya da ya aikowa Freedom Radio.

Baba Jibo ya ce, hutun na su zai fara a ranar 23 ga watan da muke ciki kuma zai ƙare a ranar 3 ga watan Oktoba na wannan shekara.

“La’akari da doka ta kundin tsarin babbar kotun jihar kano ta shekarar 2021, wadda ta bai wa babban jojin Kano mai shari’a Nura Sagir Umar dama na bai wa manyan kutanan hutu” inji Baba Jibo.

Mai magana da yawun kotunan ya kuma ce” an samar da wasu alƙalai na shirin ko-ta-kwana da suka haɗar da babban jojin Kano mai shari’a Nura Sagir Ibrahim da mai shari’a Dije Abdu Aboki sai Sunusi Ado Ma’aji  da za su zauna a kotuna yayin wannan hutu” cewar Baba Jibo.

Baba Jibo Ibrhaim ya ce, ana sanar da dukkanin lauyoyin gwamnati da masu zaman kan su, har ma da masu shigar da ƙara da su san da wannan hutu.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!