Labarai
Mutane 39 sun rasu yayin da wasu da dama suka jikkata a hatsarin jiragen kasan Spain

Akalla Mutane 39 sun rasa ransu sannan wasu da dama sun jikkata bayan wasu jiragen ƙasa biyu sun yi taho mu gama da juna a kudancin Sifaniya.
Ɗaya daga cikin jiragen na kan hanyarsa ne daga Malaga zuwa Madrid inda ya kauce wa hanyarsa, ya koma kan ɗaya layin dogon da a nan ne suka yi karo da wani jirgin da ke tafiya a kan layin dogon.
Firaiministan Sifaniya, Pedro Sanchez ya bayyana lamarin a matsayin abin tashin hankali da kaɗuwa.
Ministan harkokin sufuri na ƙasar ya ce har yanzu ba a san dalilin da ya sa jirgin ya kauce daga hanyarsa ba.
Rahotonni sun bayyana cewa, tuni masu aikin ceto suka kai wa ga waɗanda suka makale a cikin jirgin na wahala saboda yadda jiragen suka lotse.
You must be logged in to post a comment Login