Connect with us

Ƙetare

Mutane 66 sun mutu a harin da mayaƙan ƙungiyar ADF suka kai Demokradiyyar Congo

Published

on

Aƙalla mutane 66 ne suka mutu a wani hari da mayaƙan ƙungiyar ADF mai suka kai kan jama’ar yankin Irumu na gabashin jamhuriyyar Demokradiyyar Congo mai maƙwabtaka da Uganda.

 

Majiyoyi sun bayyana cewa mayaƙan na ADF sun kai harin ne a Asabar ɗin ƙarshen mako kuma dukkanin mutanen da suka kashe fararen hula ne da basu ji ba basu gani ba.

 

Harin ya zo ne a dai dai lokacin da ake ganin lafawar tashe-tashen hankula a yankin na gabashi gab da iyakar ƙasar da Rwanda sakamakon janyewar mayaƙan M23.

 

Kakakin shirin Majalisar ɗinkin duniya a Congo Jean Tobie Okala, ya ce hare-haren na ADF sun ta’azzara a sassan gabashin ƙasar, inda a tsakanin ranar Alhamis zuwa Juma’ar da ta gabata mayaƙan suka kashe mutane aƙalla 30.

 

A wata tattaunawar sa da AP Okala ya ce bayanan da suka tattara a yankunan da ADF ta kai hare-hare ya nuna cewa an kashe fararen hular da yawansu ya kai 31 zuwa 66 a ƴan tsakanin nan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!