Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Watford ta Sallami Claudio Ranieri daga aikin horas da kungiyar

Published

on

Watford Ta Sallami Claudio Ranieri Daga Aikin Horas da ‘Yan Wasan Kungiyar

Kungiyar kwallon kafa ta Watford ta sallami mai horas da ‘yan wasan kungiyar, Claudio Ranieri bayanda ya jagoranceta wasanni 14 a kasa da watanni 4.

Tun bayan da mahukuntan kungiyar ta Watford suka nada Ranieri mai shekaru 70 dan asalin kasar Italiya jan ragamar kungiyar a ranar 4 ga watan Oktoban shekarar 2021 maki bakwai kacal ya iya ciwowa a gasar Pirimiyar kasar Ingila.

Ko a ranar Juma’ar data gabata Watford karkashin jagorancin Ranieri tayi rashin nasara a hannun kungiyar kwallon kafa ta Norwich City da ci Uku da nema, wanda hakan yasa ta koma cikin kungiyoyi ukun karshen teburin gasar Pirimiya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!