Connect with us

Labarai

Mutane 80 daga cikin masu ibada da aka sace a a Kurmin Wali sun koma gida

Published

on

Rundunar ‘ƴan sandan jihar Kaduna ta ce mutum 80 daga cikin masu ibada da aka sace sun koma gida, makonni bayan aukuwar lamarin.

 

Mutanen na daga cikin mutum 177 da aka yi garkuwa da su daga coci uku a Kurmin Wali, wani yanki dake Kajuru a arewacin jihar Kaduna.

 

Mai magana da yawun  ’yan sandan jihar, DSP Mansur Hassan, ya shaida wa BBC cewa mutanen sun tsere ne a ranar da aka sace su, a lokacin da ’yan bindigar ke ƙoƙarin kwashe su zuwa wani wuri.

 

A cewar sa bayan tserewar, sun ɓuya a wasu ƙauyuka na kusa tsawon makonni, inda suka jira har sai sun ga yanayin wurin ba matsala kafin su koma gida.

 

Ya ƙara da cewa jami’an tsaro na ci gaba da ƙoƙarin ceto sauran mutum 87 da har yanzu ke hannun masu garkuwa da mutanen.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!