Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Zamfara : ‘Yan bindiga sun sace Kansila

Published

on

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun sace mutane shida cikinsu har da tsohon kansila mai wakiltar mazabar Wanke a birnin Gusau dake jihar Zamfara Salmanu Ahmad.

Sauran sun hada da Aminu Sarki da Lawalli mai chemist da Yusha Jangebe da Malama Nafisa da kuma Alhaji Anas.

Wani dan uwan daya daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su Muhammad Bashari Jangebe, ya bayyana wa manema labarai cewa ‘yan bindigar sun shiga kauyen cikin dare inda suka shiga gidajen mutanen da suka yi garkuwa da su.

Bashari ya cemafi-akasarin wadanda aka sace din ‘yan kauwa ne, inda masu garkuwa da mutanen suka bukaci kudin fansa kimanin naira miliyan sittin bayan tattaunawa da su ta wayar tarho.

Tuni dai rundunar ‘yan sandan Jihar Zamfara ta bakin mai magana da yawunta SP Muhammed Shehu ta ce ta baza jami’anta domin nemo mutanen da aka sace.a a fadin jihar baki-daya.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!