Connect with us

Labarai

Mutane da dama sun rasa ransu a sabon rikicin kabilanci a jihar Filato

Published

on

Mutane da dama ne a ka kashe a wani sabon rikicin kabilanci daya barke a Yelwan Zangam, dake karamar hukumar Jos ta Arewa, a jihar Plateau.

Rahotanni sun tabbatar dacewar an kona gidaje da dama, a sabon rikicin da ya barke a ranar 24 ga Agusta, mako daya bayan kashe wasu Fulani matafiya su 27, a Gada Biyu zuwa Rukuba, ta jihar.

Wani shaidar gani da ido ya shaidawa jaridar Daily Trust, cewar sama da mutane talatin ne aka kashe a sabon rikicin.

Rikicin ya biyo bayan gargadin da rundunar sojin kasar nan, ta ‘Operation Safe Haven’ mai kokarin wanzar da zaman lafiya a jihohin, Bauchi da Kaduna, tayi na cewar wasu daga cikin bata gari na kokarin sake kitsawa tare da tayar da rikici a jihar ta Plateau.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!