Labarai
Mutane miliyan 60 ne a Najeriya ke fama da lalurar kwakwalwa
Binciken likitocin kwakwalwa ya gano cewa, halin da yan Najeriya ke ciki na rashin kudi a hannunsu zai iya haifarwa da yawa daga cikinsu cutar damuwa ko kuma lalurar kwakwalwa.
A cewar masana lafiyar kwakwalwa, sama da mutane miliyan 60 yan Najeriya ne ke fama da lalurar kwakwalwa, kuma kaso goma daga cikinsu ne kadai ke iya samun kulawa.
Kan wannan batu ne muka tuntubi masanin halayyar dan adam na jami’ar Bayero a nan Kano Farfesa Sani Lawal Malumfashi ga kuma karin bayanin da ya yiwa wakiliyarmu Hafsat Ibrahim Kawo.
Farfesa Sani Lawal Malumfashi kenan masanin halayyar dan adam na jami’ar Bayero da ke nan Kano, da ya yi karin haske kan yadda rashin kudi da ake fuskan a yanzu zai iya haifar da lalurar kwakwalwa ga wasu yan Najeriya.
Rahoton: Hafsa Ibrahim Kawo
You must be logged in to post a comment Login