Labarai
Mutane na da ‘yancin daukar hoto ko bidiyon ‘yan sanda yayin gudanar da aiki
Hukumar ‘yan sandan Najeriya ta ce yan ƙasar na da damar ɗaukar bidiyo da hotunan ‘yan sanda a lokacin da suke gudanar da aiki.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan ƙasar, Muyiwa Adejobi ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X ranar Alhamis.
Adejobi na mayar da martani ne kan saƙon da wani mai amfani da shafin ya wallafa da ya ce ‘yan sanda sun tatse shi naira 10,000 saboda bidiyon da ya ɗauke su a lokaci da suke binciken ababen hawa.
Kakakin rundunar ya ce ba laifi ba ne ɗaukar hoto da bidiyon ‘yan sanda a lokacin da suke bakin aiki.
Ya ƙara da cewa rundunar ta sha gaya wa mutanen cewa babu laifi ɗaukar bidiyo da hotunan ‘yan sandan da ke bakin aikin.
Mista Adejobi ya ce duk wanda ‘yan sanda suka ci zarafinsa saboda ɗaukarsu bidiyo ko hoto su kai rahoto ga hukumar ‘yan sanda.
Cikin sakonsa na X da ya wallafa, mista Adejobi ya ce ”ya kama kowane ɗan sanda ya sani cewa ba laifi ba ne ɗaukar bidiyo ko hotunansu a lokacin da suke bakin aiki”.
“Waɗanda ke cin zarafin masu ɗaukarsu hoto ko bidiyo saboda wannan, su daina”.
You must be logged in to post a comment Login