Labarai
Mutane sama da dubu goma ne da ambaliyar ruwa ya shafa suka samu tallafi daga Gwamnatin tarayya
- Gwamnatin Nigeriya ta ce, sama da mutane dubu goma sha uku ne suka ci gajiyar tallafin rage radadin.
- babban sakataren ma’aikatar jin kai da walwalar jama’a ta kasar Dakta Nasir Gwarzo ya fitar.
- jahohin da su ka ci gajiyar tallafin sun hadar da Jihar Amabra, Bayelsa, Katsina, Kogi, Benue, Nasarawa, da kuma Kwara.
Gwamnatin Nigeriya ta ce, ‘sama da mutane dubu goma sha uku ne suka ci gajiyar tallafin rage radadin ambaliyar ruwa a fadin kasar’.
Hakan na cikin wata sanarwa da babban sakataren ma’aikatar jin kai da walwalar jama’a ta kasar Dakta Nasir Gwarzo ya fitar a jiya talata.
Sanarwar ta kara da cewa ‘jahohin da su ka ci gajiyar tallafin sun hadar da Jihar Amabra, Bayelsa, Katsina, Kogi, Benue, Nasarawa, da kuma Kwara’.
‘Sauran su ne, jihar Niger, Kebbi, Sokoto, Jigawa, Bauchi, Delta, Rivers, Adamawa, da kuma Jihar Yobe’.
‘Kayayyakin da aka raba sun hadar da kayan abinci da sutura sai kuma matsuguni da dai sauransu’.
Rahoton: Nura Bello
You must be logged in to post a comment Login