Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Mutane sama da dubu dari ne zasu iya samun aikin a sana’ar dogaro da kai a Kano duk shekara: Kungiya

Published

on

  • A kalla matasa dubu dari biyar ne za su samu aikin yi a kowacce shekara a Kano, matukar zasu mayar da hankali wajen sana’o’in dogaro da kai.
  • Shugaban kungiyar Kungiyar rajin samar da kyakyawar tarbiyya da ci gaban matasa ta ce Malam Nura Ali Abdullahi Medille ne.
  • Raina kananan sana’o’i da yin shaye-shaye tsakanin matasana, na daga ciki abubuwan da ke kara ta’azzara masu zaman banza.
  • Ya kuma bayyana hakan da barazana ga matasa

 

Kungiyar rajin samar da kyakyawar tarbiyya da ci gaban matasa ta ce, a kalla matasa dubu dari biyar ne za su samu aikin yi a kowacce shekara a Kano, matukar zasu mayar da hankali wajen sana’o’in dogaro da kai.

Shugaban kungiyar Malam Nura Ali Abdullahi Medille ne ya bayyana hakan, a zantawarsa da Freedom Radio a safiyar yau.

Tattaunawar dai ta mayar da hankali ne kan tushen gurbacewar tarbiyyar matasa da matsalolin da hakan ke haifarwa.

Ya kuma ce, ‘raina kananan sana’o’i da yin shaye-shaye tsakanin matasana, na daga ciki abubuwan da ke kawo koma baya wajan ci gaban matasa a wanna lokaci’.

Malam Nura Ali abdullahi Medille ya ce, ‘babbar barazanar gurbacewar tarbiyyar matasa bai wuce yadda za ta haifar da rashin tsaro da zaman lafiya a tsakanin al’umma’.

Rahoton: Aisha Aliyu Getso

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!