Labaran Kano
Mutanen Ja’en za su yi karar majalisar dokokin Kano
Kungiyar cigaban al’ummar unguwar Ja’en ta nemi majalisar dokokin jihar Kano kan ta gabatar da mutumin da aka ce daga unguwar ta Ja’en yake, ya shigar da korafi kan sarkin Kano a majalisar.
Cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar cigaban mutanen unguwar Ja’en Kwamaret Tamim Bala Ja’en da sakataren sa Kwamaret Ibrahim Yahya Ja’en ta yi kira da babbar murya ga majalisar dokokin jihar Kano kan ta gabatar da mutumin a gabanta idan har akwai shi, ko kuma su garzaya gaban kotu.
Wannan sanarwa dai ta biyo bayan wani zama da masu ruwa da tsaki a unguwar suka gudanar a yau jumu’a inda suka yi Allah-wadai da abinda mutumin da aka kira da suna Muhammad Mukhtar yayi na shigar da korafi ga majalisar dokokin Kanon kan mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II.
Al’ummar unguwar ta Ja’en sun ce ba za su lamunci wannan batu ba, kuma sam ba da yawunsu akayi ba.
A karshe sanarwar ta ce al’umar Ja’en mutane ne dake biyayya ga Masarautar Kano da kuma gwamnatin Kano.
You must be logged in to post a comment Login