Labarai
Mutum 1 ya rasu sakamakon ruftowar gini a Kirikasamma

Majalisar ƙaramar hukumar Kirikasamma ta jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar mutum ɗaya da kuma jikkatar wasu bakwai sakamakon rushewar wani gini a yankin.
Jami’in yaɗa labaran hukumar, Musa Muhammad, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai.
Ya ce lamarin ya faru ne bayan ruwan sama mai yawa da aka samu a Kirikasamma da kewaye, inda ginin ya rushe a ƙauyen Kabak da tsakar dare ranar juma’a.
Muhammad ya bayyana cewa mutum bakwai sun jikkata sosai, yayin da mutum ɗaya ya rasa ransa.
Cikin waɗanda suka jikkata, biyar an kwantar da su a asibiti don samun kulawa, yayin da aka sallami sauran biyu bayan samun magani.
You must be logged in to post a comment Login