Ƙetare
Mutum 16 sun mutu yayin da 400 suka jikkata a zanga-zangar Kenya

Rahotanni sun bayyana cewa mutane 16 sun mutu, yayin da 400 kuma suka jikkata, inda jami’an tsaro suka kama karin matasa 61 a zanga-zangar da aka gudanar a faɗin kasar Kenya jiya Laraba, domin tunawa da shekara daya da zanga-zangar adawa da ta biyo bayan ƙarin haraji da gwamnatin ƙasar ta yi, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.
Hukumar kare haƙƙin Dan-adam ta ƙasar KNCHR ta ce, ta tabbatar da mutuwar mutum 8 da harbin bindiga ya kashe su a wuraren da suka hada da Machakos da Makueni da Kiambu sai Nakuru da kuma Nyandarua.
Sai dai Kamfanin dillancin labarai na Reuters, ya bayyana cewa Amnesty Kenya ta ce, mutum 16 ne suka mutu.
An samu hargitsi da tarzoma a wurare da dama, ciki har da toshe hanyoyi tare da yin jifa da Duwatsu da amfani da hayaki mai sa hawaye da ruwa zafi da kuma yunkurin mamaye Majalisar dokokin ƙasar.
BBC ta ruwaito cewa, hukumar sadarwa dai ta hana yada shirye-shirye kai tsaye, amma gidajen rediyo da talabijin sun ƙi bin umarnin, inda suka ci gaba da yada zanga-zangar a kafafensu na sada zumunta.
You must be logged in to post a comment Login