Labarai
Mutume 176 sun mutu sakamakon cutar zazzaɓin Lassa- NCDC

Hukumar kula tare da dakile cutuka masu yaduwa ta Najeriya NCDC, ta tabbatar da mutuwar mutume 176 sakamakon cutar zazzaɓin Lassa a jihohi 21 cikin watanni 10.
NCDC ta ce adadin mutanen da cutar ke kashewa ya ƙaru daga kashi 16.6 cikin 100 a 2024 zuwa 18.4 a 2025 duk da raguwar masu kamuwa da cutar a tsakanin.
Hukumar ta ɗora alhakin mutuwar kan rashin kai rahoto da wuri, da rashin neman taimakaon likitoci.
Haka kuma, hukumar ta bayyana cewa, ƙarin mutane 955 ne daga cikin 8,367 da aka gwada suka kamu da cutar ta Lassa a 2025, inda jihohin Ondo, Bauchi, Edo, Taraba suka zama cibiyar cutar da kashi 88 cikin 100 na duka mutanen.
You must be logged in to post a comment Login