Labarai
Babu alaka tsakanin Mutuwa a Turmutsutsu da mulkin Tinubu- Gwamnatin tarayya
Gwamnatin tarayya, ta musanta cewa, turmutsutsun da yayi sanadiyyar hallaka mutane da kuma raunata wasu da dama na da alaka da salon mulkin shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Mininstan yada labarai Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan tare da yin gargadi ga ‘yan siyasa da su daina alakanta iftila’in da aka samu na turmutsutsu a yayin rabon tallafin abinci a Oyo da Anambra da kuma Abuja.
Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da babban mataimaka na musamman ga ministan Rabiu Ibrahim, ya fitar.
Sanarwar, ta kuma bukaci duk masu shirin bayar da irin wannan tallafi da su rika daukar matakan da za su hana faruwar irin wannan iftila’i.
Ministan, ya kuma, mika sakon jaje da ta’aziyyarsa ga dangin mutane fiye da saba’in da suka rasu wanda kusan arba’in daga cikin kananan yara ne.
A baya-bayan nan ne dai dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Labour a zaben da ya gabata Peter Obi, ya zargi salon shugabancin Bola Ahmed Tinubu, da yin musabbanbin jefa ‘yan Najeriya cikin matsanancin hali.
You must be logged in to post a comment Login