Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Mutuwar Martins: An gurfanar da NFF da LMC gaban kotu

Published

on

Mahaifan tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Nasarawa United da ya mutu Chineme Martins sun shigar da karar hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF da kamfanin shirya gasar League LMC da kuma Nasarawa United a gaban kotu.

Chineme Martins ya fadi ne a filin wasa yayin da yake bugawa kungiyar tashi Nasarawa United wasa a karawarsu da Katsina United a garin Lafia dake a jihar ta Nasarawa.

Dan wasan mai shekara 23 ya mutu ne a ranar takwas ga watan Maris din shekarar da ta gabata ta 2020 bayan faduwarsa a filin wasan.

Iyayen Martins dai sun bukaci kungiyar ta biyasu kudin Diyya naira miliyan dari da ashirin sakamakon mutuwar dan nasu.

Haka zalika kungiyar magoya bayan ‘yan wasa ta duniya wato Fifpro ta ce, “Kawo yanzu Nasarawa United ta gaza mikawa iyayen Martins takardun inshorarsa tare da na kwantiraginsa da kungiyar kuma har ila yau babu wani taimako daga kungiyar ko NFF.”

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!