Connect with us

Kowane Gauta

Na amince ayi sulhu tsakanina da Kwankwaso – Ambasada Aminu Wali

Published

on

Guda daga cikin jagororin jam’iyyar PDP a jihar Kano Ambasada Aminu Wali ya ce, ya amince ayi sulhu tsakaninsa da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso jagoran darikar kwankwasiyya amma bisa sharadi.

Ambasada Aminu Wali yace daga cikin sharadin shine dole ne abi doran tsarin mulkin jam’iyyar PDP wanda jama’ar da aka samu abasu damar zabar wadanda suke so amma ba shugaban jam’iyya ko wani ya yi musu kutse ba wajen dagewa kan  wanda zasu zaba.

Aminu Wali ya bayyana hakan ne a cikin shirin kowanne Gauta na tashar Freedom Radiyo dake nan ta cikin shirin Kowanne Gauta.

Aminu Wali yace matukar jama’a suna sanka kuma sun zabeka ko ba kada ko sisi dole ayi da kai domin hakan shine Demokradiyya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 333,342 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!