Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Na koma aikin gini da sharar kwata – Mamallakin makaranta a Kano

Published

on

Matsalar rufe makarantu da aka yi ciki har da masu zaman kansu a Kano ya tilastawa wani shugaban makaranta mai zaman kanta  shekaru hamsin da biyar a duniya fara neman aikin sharar kwata da aikin gini sakamakon mawuyacin halin da ya tsinci kansa na rashin kudi da aikin yi.

Tun da fari mutumin mai suna Malam Hussain Abdulhamid Muhammad ya shaidawa wakilin gidan Radio Freedom Abdulkarim Muhammad Tukuntawa cewa ya dauki wannan matakin ne sakamakon bashida wata sana’a da yake gudanarwa a yanzu.

Malam Hussain ya kara da cewa yanada iyali ga kuma  tarin ‘ya’ya da yake dasu wanda hakan ya tilasta masa daukar wannan mataki domin rufawa kansa asiri dana iyalinsa.

Hussain Abdulhamid ya kuma shawarci gwamnatin jihar Kano da ta kawowa malaman makarantu masu zaman kansu dauki sakamakon mawuyacin halinda suke ciki a yanzu.

Ya kara da cewa rayuwar malaman makarantu masu zaman kansu a yanzu na cikin garari, saboda ci gaba

da rufe makarantu da ake yi sakamakon bullur annobar cutar covid 19.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!