Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Sabon Kwamishina ya umarci ‘yan sandan Kano su kauce wa karabar cin Hanci

Published

on

Sabon kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano Muhammad Usaini Gumel ya gargadi jami’an rundunar da su kauce wa aikata duk wani laifin karbar cin hanci da rashawa domin ko kadan bazai lamunci abunda zai batawa ‘yan sanda suna ba.

Kwamishinan, ya bayyana hakan ne yau Talata lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan fara kama aiki da ya yi a matsayin sabon kwamishinan ‘yan sanda.

Muhammad Usaini Gumel ya kara da cewa rundunar ‘yan sandan Jihar Kano za ta rika amfani da sabbin dabaru na zamani wajen cafke duk wasu masu aikata muggan laifuka a fadin jihar Kano   domin tabbatarda tsaro da zaman lafiya.

Ya kuma bukaci hadin kan sauran hukumomin tsaro da  kungiyoyin al’umma da kuma ‘yan sandan cikin al’umma da su ci gaba da bai wa rundunar yan sandan  hadin kai domin magance matsalar  tabarbarewar tsaro.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!