Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Na fara sayen Zinare don magance matsalar tsaro – Gwamnan Zamfara

Published

on

Gwamnatin jihar Zamfara ta fara sayen ma’adanan zinare daga hannun masu haƙowa a jihar.
Gwamnan jihar Zamfara Muhammad Bello Matawalle ne ya bayyana hakan, inda ya ce hakan zai taimaka wajen magance matsalar tsaro a jihar.
Matawalle ya ce, Allah ya albarkaci jihar da ma’adanai da dama amma an barsu sasakai babu tsari, kuma gwamnatin jihar ba zata lamunci hakan ba.
Zai tabbatar al’ummar jihar sun amfana da albarkar da Allah ya yiwa jihar.
Gwamnan ya kuma koka cewa, wasu idan sun fita waje sun sayar da zinare suna dawowa jihar da makamai, lamarin da ke ta’azzara matsalar tsaron jihar.
Yanzu babu wani kamfani da zai kara sayen zinaren ya fita da shi, gwamnati zata rika saya ta ajiye shi ya zama mallakin al’ummar jihar Zamfara inji gwamnan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!