Connect with us

Labarai

Na karbi mulki ne yayin da Hukumar Fansho ke dab da durkushewa- Gwamna Umar Namadi

Published

on

Gwamnan jihar Jigawa Malam Umar Namadi, ya ce, ya karbi mulkin jihar ne a dai-dai lokacin da hukumar biyan fansho ta jihar ke daf da durkushewa sabo da rashin kudi.

 

Gwamnan ya bayyana haka ne lokacin da ya ke karbar kyautar girmamawa daga kungiyar ‘yan fashio ta kasa ta hanun shugaban ma’aikata a gidan gwamnatin jihar da ke birnin Dutse.

 

Ya ce, a kasa da shekara biyu kadai gwamantinsa ta saka kudi  a asusun na yan fansho sama da Naira miliyan dubu 7 kafin ya farfado daga halin durkushewa.

 

Haka kuma, ya kara da cewa tini gwamnatin jihar ta yi wa dokar asusun kwaskwarima domin tabbatar da dorewarsa tare da ci gaba da biyan masu hakki hakkokinsu a kan lokaci.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!