Labaran Wasanni
Na warware daga jinyar rauni da nake- Toni Kross
Bayan fama da jinyar raunin da ya yi, dan wasan tsakiya na kasar Jamus da kungiyar Real Madrid Toni Kroos, ya warware daga jinyar raunin da ya tafi.
Rabon da dan wasa Toni Kroos ya buga wasa tun da aka kammala gasar Euro 2020 a watan Yuni da Yulin shekarar 2021.
Kroos mai shekara 31, ya wallafa jindadinsa a shafin sa na sada zuminci kan warwarewar da ya yi daga jinyar da yai fama da it.
Ya kara da cewa “na shafe watanni cikin yanayin wahala lokacin da nake buga wa Madrid da Jamus wasa sai daga baya na samu damar amfani da magunguna don magance ciwon,”
“Na yi farin ciki saboda a yau na sami damar yin horo na uku tare da kungiyar Real Madrid”.
Dan wasan ya kuma ce ya na fatan zai fafata a wasan da Madrid za ta kara da Sheriff ta kasar Moldova a gasar cin kofin zakarun Turai Champions League a ranar Talata 28 ga watan Satumbar 2021.
Sai dai ya ce shawarar bashi damar hakan tana akan mai horar da kungiyar Carlo Ancelotti
You must be logged in to post a comment Login