Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Addini

Indai ba za a yi mun adalci ba, na yi laifi, kawai ku hukunta ni – Malam Abduljabbar

Published

on

Sheikh Abduljabbar Kabara ya bayyana cewa, Indai ba za a dubi Ubangiji ba, to kawai a hukunta shi yayi laifi.

Malamin ya bayyana hakan ne, yayin da yake amsa tambayar da Malam Kabir Bashir Abdulhamid ya yi masa.

Malamin ya ce, waɗannan matsalolin ba nasa ne shi kaɗai ba, batutuwa ne da aka ci zarafin addini, wanda shi kuma yake ƙoƙarin korewa.

Malam Abduljabbar ya ci gaba da cewa, yayi zaton za a yi wannan zaman ne da gaskiya saboda kishin Manzon tsira, amma abin ba haka bane.

Tun zagaye na biyu, ya zargi shirin muƙabalar da zalunci, inda Kwamishinan addini ya yi masa jan kunne.

Sai dai ya ƙara tabbatarwa yana mai cewa, akwai zalunci a cikin tsarin zaman.

Malam Abduljabbar ya ƙara da cewa, wannan matsalolin suna ta haifar da ridda a duniyar musulunci, mutane na barin musulunci ba adadi a duniya.

A don haka yake roƙon Malaman da su ji tsoron Allah a tsaya a duba lamarin daki-daki don a ceci musulunci.

Malamin ya kuma ce, kusan litattafai 500 ya zo da su, amma ya ga abin ba zai yiwu ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!