Labarai
NAFDAC ta kama dan wasan kwallon kafa bisa zarginsa da raba wa mutane kayan maye

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Najeriya NAFDAC, ta kama wani dan wasan kwallon kafa mai suna Mista Ikechukwu Elijah a unguwar Apo-Waru da ke birnin tarayya Abuja bisa laifin rarraba sinadarai masu hadari ga mutane.
Hakan na cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mataimakin daraktan hulda da jama’a na hukumar Mista Adegboyega Osiyemi, da ya fitar a safiyar yau Juma’a.
A cewar sanarwar, ta NAFDAC ta ce wanda ake zargin yana gudanar da wata haramtacciyar masana’anta ne a cikin wani gida da ke yankin, kuma ya yi kaurin suna wajen yin jabun wasu nau’in sinadarai da ka iya cutar da rayuwar al’ummar kasar nan
Hukumar NAFDAC ta sha yin gargadin cewa irin wadannan abubuwa na sanya ‘yan kasa su shiga cikin abubuwa masu hadari, baya ga barazana ga harkokin tsaro a kasa.
You must be logged in to post a comment Login