Kiwon Lafiya
NAFDAC: ta gargadi jami’an lafiya da su kula da nau’in rigakafin amai da gudawa na bogi
Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC ta bukaci al’ummar kasar nan musamman masu ruwa da tsaki a harkar lafiya da su kula da nau’in wani rigakafin cutar Amai da gudawa na bogi mai suna ‘Dukoral Oral Cholera vaccine’ wanda tuni ya mamaye kasuwannin kasar Bangladesh.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugabar hukumar Farfesa Moji Adeyeye.
A cewar shugabar hukumar ta NAFDAC nau’in rigakafin na Dukoral vaccine akwai bayanai da aka rubuta a jikin kwalinsa da harsunan turanci da faransanci.
Shugabar hukumar ta NAFDAC ta kara da cewa hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta yi gwajin rigakafin kuma ta gano matsalolin da ke tattare da shi.
Farfesa Moji Adeyeye ta kuma ce ya zama wajibi ta dau wannan mataki don fadakar da jama’a musamman masu ruwa da tsaki a harkar lafiya.