Labarai
Nagartar aiki: An fara tantance ma’aikatan sharar titi a Kano
Gwamnatin jihar Kano ta fara tantance masu aikin shara a titunan jihar a wani yunƙuri na tabbatar da ma’aikatan da aka ɗauka bisa ƙa’ida.
Kwamishinan muhalli da Nasiru Sule Garo ne
ya bayyana hakan a yau jim kadan bayan kaddamar da kwamitin tantancewar a hukumar kula da kwashe shara REMASAB.
Kwamishinan ya ce, an baiwa kwamitin kwanaki biyar ya kammala aikinsa tare da fitar da cikakken rahoto kan yadda za a ci gaba da gudanar da harkokin tsaftar muhalli.
Don haka ya umarci mambobin kwamitin da su tabbatar da amincewar da aka yi musu don ganin an kammala aikin da aka ba su a kan lokaci.
Da yake jawabi shugaban kwamitin wanda kuma shine mai baiwa gwamna shawara kan tsaftar muhalli Injiniya Abdullahi shehu Bichi ya ce, a shirye suke su sauke wannan aiki da ba tare da wani tsoro ba, sai dai ya yi kira ga masu shara a jihar da su zo tare da duk wasu takardun shaida domin tantance su.
Bayanin hakan na cikin sanarwar da daraktan yada labaran ma’aikatar muhalli Ismail Garba Gwammaja ya fitar.
You must be logged in to post a comment Login