Connect with us

Labarai

NAHCON ta kayyade kudin Hajjin bana

Published

on

Hukumar aikin hajji ta Nijeriya NAHCON ta bayyana kudin da maniyyata aikin hajjin bana zasu biya a hukumance.

Ta cikin wata takarda mai dauke da sa hannun mataimakiyar daraktar yada labaran hukumar Fatima Sanda Usara ta sanyawa hannu, ta ce “an sanya kudaden ne a matakai daban daban na shiyyoyin kasarnan”.

Inda mataki mafi kasa zasu biya naira miliyan 4 da dubu dari 6 da 79, yayinda mafi kololuwa zasu biya naira miliyan 4 da dubu dari 8 da 99.

Wannan dai na zama kari akan kudaden da a baya aka tsammaci hukumar zata sanya, wadda ta ce an samu karin ne sakamakon hauhawar farashin dalar da ake cigaba da fuskanta a kasarnan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!