Connect with us

Labarai

NAHCON ta  sha alwashin fara shirye-shiryen aikin Hajjin bana a kan lokaci

Published

on

Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Najeriya NAHCON ta  jaddada kudirinta na fara shirye-shiryen aikin Hajjin shekarar 2026 a kan lokaci.

 

Shugaban hukumar, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da Mai taimaka masa na Musamman kan Harkokin Yaɗa Labarai, Ahmad Mu’azu, ya fitar a daren jiya Lahadi a Abuja.

 

Ya ce, hukumar na aiki daidai da manufofin Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu,

 

Haka kuma, ya kara da cewa, Shugaban NAHCON ya kuma amince da tura babbar tawagar shugabanni zuwa Masarautar Saudiyya, domin kammala da karɓar dukkan shirye-shiryen masauki da suka rage a Makkah, tare da kauce wa duk wata tangarda a aiki.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!