Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamna Matawalle ya bukaci EFCC ta binciki jami’ai da ministocin shugaba Buhari

Published

on

Gwamnan jihar Zamfara Muhammad Bello Matawalle, ya bukaci hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC da ta fara bincike a kan jami’an gwamnatin shugaba Buhari da ministocinsa, da zarar sun sauka daga mulki.

Matawalle na wadannan kalamai ne a matsayin martani kan sanarwar shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa da ke cewa sun tura wa gwamnonin da ke barin mulki da kwamishinoni gayyata da zarar sun kammala miƙa mulki, domin binciken su.

Gwamnan ya ce irin wannan bincike bai kamata ya tsaya a kan gwamnoni da kwamishinoni ba, ya kamata a hada har da masu aiki a fadar shugaban kasa.

Haka kuma, ya shawarci EFCC ta tabbatar ba ta sanya siyasa ko son rai a binciken nata ba, domin hukunta duk wanda aka samu da laifi.

Gwamnan na jihar Zamfara dai, na daga cikin gwamnonin da suka karbi wasikar da EFCC ta aike wa gwamnoni na bincikarsu bayan sauka daga mulki.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!