Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Najeriya ba ta cikin jerin ƙasashen da ake cin zarafin ɗan jarida – Abubakar Malami

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ce, Najeriya ba ta cikin jerin ƙasashen da ake cin zarafin ƴan jarida a yanzu.

Ministan shari’a kuma atoni janar na ƙasa Abubakar Malami SAN ne ya bayyana hakan a zantawar sa da Freedom Radio.

Yayi bayanin ne ta bakin mai magana yawun sa Umar Jibril Gwandu a wani ɓangare na bikin ranar yaƙi da cin zarafin ƴan jarida da ake gudanarwa a ranar 2 ga watan Nuwamba.

“Rahotan shekarar 2020 ya nuna cewa Najeriya ce ƙasa ta farko da ta fita daga jerin ƙasashe da ke cin zarafin ƴan jarida cikin ƙasashe irin su Somalia sudan da sauran su”.

“A ƙoƙarin da gwamnati ke yi na rage cunkoso a gidajen gyaran hali, ƴan jarida sune gaba wajen faɗakarwa kan hana aikata laifuka, da kuma ɗan aka doka ta samun ƴancin bayanai”.

Ya ci gaba da cewa “Ƴan jarida a Najeriya na cikin ƙasashen da ake basu dama su gudanar da ayyukan su, dalilin kenan da ya a yanzu ake ganin yawaitar buɗe kafafen yaɗa labarai a ƙasar”.

Sai dai yayin da ministan ke wannan bayani rahoton UNESCO ya gano cewa tsakanin shekarar 2006 zuwa 2020, an kashe ƴan jarida sama da 1,200 sanadiyyar aikin tattara bayanai.

Yayin da a cikin kaso 9 cikin 100 na waɗanda suka kashe ƴan jarida ba a kai ga hukunta su ba.

A cewar UNESCO cin zarafin mata ƴan jarida ta hanyar internet ya karu da kashi 73 cikin 100 musamman ta ɓangaren yi musu barazana.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!