Connect with us

Kiwon Lafiya

Tallafi: An fara tantance masu bukata ta musamman don basu kulawar lafiya kyauta a Kano

Published

on

Hukumar taimakekeniyar lafiya ta jihar Kano ta fara yiwa masu bukata ta musamman rijistar tallafin lafiya kyauta, a wani mataki na inganta rayuwarsu da ta yaransu.

Shugabar hukumar Dakta Halima Muhammad Mijinyawa ce ta kaddamar da shirin a Litinin din nan.

Ta ce shirin wani yunkuri ne da zai takaitawa masu bukata ta musamman wahalhalun neman lafiya da kuma sayan magunguna.

A cewarta gwamnatin jihar kano zata ci gaba da bai wa masu bukata ta musamman tallafin lafiya tare da daidaita su da suran mutanen da suke gudanar da rayuwarsu kamar takwarorinsu na duniya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,433 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!