Kasuwanci
Najeriya da sauran kasashen afurka na fuskantar karancin abinci – Zainab Ahmed
Gwamnatin tarayya ta ce Najeriya da sauran kasashen afurka na cikin tsaka mai wuya sakamakon rashin isashshen abinci da zai biya bukatun al’ummar ta tsawon lokaci.
Ministan kudi, kasafi da tsare-tsare Zainab Ahmed ce ta bayyana haka yayin wani taro kan samar da abinci ga nahiyar afurka wanda bankin duniya ya shirya aka gudanar ta kafar internet.
Ta ce Najeriya kamar sauran kasashen afurka tana fuskantar matsaloli masu yawa wajen samun isashshen abinci, wanda haka yana matukar barazana ga tsaro da zaman lafiyar al’ummar ta.
‘‘Mun yi imanin cewa muna da matsalar karancin abinci mai dorewa, saboda haka muna fata kamata ya yi masu ba da tallafi ga nahiyar afurka da su karkatar da akalarsu ta bangaren tallafawa harkar noma’’ inji Zainab Ahmed.
You must be logged in to post a comment Login