Connect with us

Labarai

Najeriya na iya zama daya daga manyan kasashen duniya – Khashim Shattima

Published

on

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya ce Nijeriya na da cikakken ƙarfi da damar zama ɗaya daga cikin manyan ƙasashe a duniya, matuƙar ’yan ƙasar suka rungumi haƙuri da zaman lafiya a tsakaninsu.

Shettima ya jaddada cewa ’yan Nijeriya suna da gadon tarihi guda, inda ya ce abubuwan da ke haɗa kan al’umma sun fi ƙarfin waɗanda ke neman raba su. Ya ƙara da cewa, dole ne ’yan ƙasa su fahimci cewa suna da alaƙa da juna ta hanyoyi daban-daban.

Mataimakin Shugaban Ƙasar ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a Jos, babban birnin Jihar Plateau.

Shettima, wanda ya ziyarci jihar ne domin halartar taron tarba na  Gwamna Caleb Mutfwang da wasu fitattun ’yan siyasa da suka shiga jam’iyyar APC, ya bayyana sarakunan gargajiya a matsayin ginshiƙan zaman lafiya da masu taka muhimmiyar rawa wajen daidaita al’umma.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!