Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kashim Shettima ya gana da manyan ‘yan kasuwar duniya

Published

on

A safiyar yau Alhamis ne Mataimakin shugaban Nijeriya Kashim Shettima, ya shiga ganawar sirri da shugaban gidauniyar Bill and Melinda Gates wato Bill Gates, da shugaban gudauniyar Dangote Foundation Alhaji Aliko Dangote, da mambobin kungiyar gwamnonin kasar nan a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Ganawar dai na da alaka da ziyarar da Mista Gates ya kawo kasar nan da Jamhuriyyar Nijar.

Wannan na zuwa ne awanni 72 bayan Mista Gates da Dangote sun gana da shugaban kasa Bola Tinubu ranar Litinin a fadar sa dake Villa Abuja.

Sai dai kawo wannan lokaci ba’a kai ga baiyana makasudin ganawar tasu ba.

Rahotanni dai na nunar da cewa mahalarta taron zasu duba yiyuwar yadda gidauniyar da gwamnatin tarayya zasu samar da hanyoyi da zasu amfani juna musamman a bangaren lafiya da Ilimi.

Rahoto: Ahmad Kabo Idris

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!