Labarai
Najeriya na kashe naira biliyan 60 wajen gyaran bututun man fetur a duk shekara – Lai Muhammad
Gwamnatin tarayya ta ce a duk shekara tana kashe kudi naira biliyan sittin don gyaran bututan man fetur din da bata-gari suke lalatawa a kasar nan.
Ministan yada labarai da al’adu Alhaji Lai Muhammad ne ya sanar da hakan a Abuja lokacin taron masu ruwa da tsaki kan harkokin man fetur da iskar gas, wanda aka gudanar a Abuja.
Lai Muhammad, ya ce, a duk shekara Najeriya tana asarar gangar mai dubu dari biyu a dalilin fasa bututun mai da bata-gari ke yi.
Ya kara da cewa daga watan Janairun shekarar 2019 zuwa Satumbar 2020, an lalata bututan mai guda dubu daya da dari daya da sittin da daya a Najeriya.
A na sa jawabin, ministan kula da harkokin yankin Neja-Delta Godswill Akpabio, ya ce masu zuba jari na kasashen waje da dama ne suka fice daga yankin sakamakon ayyukan tsagerun Neja-Delta.
Shi kuwa ministan muhalli Muhammad Mahmoud Abubakar cewa ya yi Najeriya tana asarar kashi 43 cikin 100 na kudaden shiga na mai sakamakon sace man da tsagerun Neja-Delta ke yi.
You must be logged in to post a comment Login