Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

‘Yan Sanda sun fafata da ‘yan fashi da makami a hanyar Maiduguri zuwa Kano

Published

on

Rundunar ‘yan sandan Jihar Jigawa ta tabbatar da cewa jami’anta sun fafata da wasu ‘yan fashi da makami da suka datse hanyar Maiduguri zuwa Kano.

Lamarin ya faru ne a daidai ofishin ‘yan sanda dake kauyen Dindibis Fanisau a karamar hukumar Dutse.

Mai magana da yawun rundunar ASP Lawan Shisu Adamu ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar.

ASP Lawan Shisu ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe tara na daren lahadin da ta gabata inda kafin zuwan ‘yan sanda sai suka harbi wani mai suna Harisu Aliyu a wuyansa da kuma kafadarsa, a yayin da suka kashe Major M S Ismail ta hanyar harbinsa da bindiga.

Ta cikin sanarwar mai magana da yawun rundunar ta Jigawa Lawan Shisu ya ce tuni jami’an sojoji da na rundunar dake yaki da masu aikata fashi da makami suka dukufa wajen neman ‘yan fashin bayan da suka tsere cikin daji lokacin faruwar lamarin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!