Kasuwanci
Najeriya ta cefanar da kamfanoninta 234 – BPE
Gwamnatin tarayya ta ce kimanin kamfanonin gwamnati 234 ne aka yi wa kwaskwarima ta hanyar mayar da su masu zaman kansu da kuma kasuwanci.
Babban daraktan hukumar cefanar da kadarorin gwamnati ta kasa, Mista Alex Okoh ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Abuja.
A cewarsa, kwanan nan kasar nan ta fita daga koma bayan tattalin arziki sakamakon illar da cutar COVID-19 ta haifar.
Ya kuma ce, kawo yanzu matsin na tattalin arzikin yana cigaba da bayyana sosai duba da yadda aka gudanar da kasafin kudi na bana.
You must be logged in to post a comment Login