Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

Najeriya ta dawo mataki na uku a yawan masu Corona a Africa

Published

on

Ya zuwa yanzu dai Najeriya ta kasance kasa ta uku da suka fi yawan masu dauke da cutar Covid-19 a nahiyar Afrika inda take biyewa kasashen Afrika ta kudu da kuma Masar.

Adadin wadanda suka kamu da cutar dai sun kai 16,658 duk da matakan yaki da wannan cuta da Najeriyar ta dauka, ya zuwa yanzu ta na da masu dauke da cutar har mutum dubu 10,885 yayin da mutum 424 suka kwanta dama sanadiyar cutar.

Mutum 5,349 ne hukumar dakile yaduwar cutuka ta Najeriya ta tabbatar sun warke tsaf daga wannan cuta a kasar.

Sai dai hukumomi a Najeriya sun ce mutum 7 ne kacal daga cikin masu jiyyar cutar ke cikin halin rai kwakwai mutu kwakwai.

To sai dai a iya cewa hakan ka iya zama babban kalubale ga Najeriyar dake ta kokarin ganin ta yaki wannan cuta a gefe guda ta fara rungumar tsarin rayuwa ta yau da kullum da corona.

A kasashe irinsu Nijar dake makwaftaka da Najeriyar, kasar da a baya ta sha gaban Najeriyar a yawan wadanda suka kamu da cutar, tuni ta rungumi tsarin rayuwa da corona ta hanyar komawa makarantu da kuma sassauta dokar kulle da ta kakaba a baya.

Hukumomin lafiya na duniya na ganin cewar akwai aiki ja a gaban kasashen nahiyar Afrika wajen ganin sun yaki cutar.

Cutar Corona dake zama cutar duniya ta kamma mutane dubu 242,969 a nahiyar Africa, ciki kuwa har da mutum dubu 6,524 da ta kashe inda ake da mutane dubu 110,735 da suka warke a nahiyar Afrika baki daya.

Kasar Amurka ce ke kan gaba a masu yawan wadanda ke dauke da cutar a duniya baki daya.

Fiye da mutum milliyan 8 ne suka kamu da cutar a duniya baki daya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!