Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

Covid-19: Kasuwancin mu ya shiga mawuyacin hali – ‘Yan Kasuwa

Published

on

Rahotonni daga jihar Nasarawa na cewa har yanzu al’umma basu murmure daga kuncin rayuwar da cutar Corona ta kawo ba, dukda cire dokar kulle da gwamnatin jihar tayi.

A Karamar Hukumar Nasarawa ta jihar Nasarawar al’amura sun gaza komawa kamar yadda suke a baya kafin bullar Corona.

Hakan ne yasa al’umomi ke ta yin korafi dangane da yadda aka samu koma baya a harkokin su na yau da kullum.

Murtala Muhammad Abubakar mai sayar da kayan masarufi ne yana daya daga cikin wadanda suka koka kan lamarin.

Da yake zantawa da wakilin mu Shehuddeen Nassarawa yace kafin bullar annobar Corona a jihar al’amura na tafiya dai-dai amma yanzu komai ya sauya.

Manazarta al’amuran yau da kullum na ganin cewa akwai abin ban tsoro anan gaba bayan wucewar Corona matukar hukumomi basu dauki kwakw-kwaran matakai game da farfado da tattalin arziki ba.

Ko a baya-bayan nan anyi hasashen miliyoyin mutane ne ka iya rasa ayyukan yi sanadiyyar cutar ta Corona.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!