Labarai
Najeriya za ta koma kan tsarin e-Visa a watan Mayu- Minista

Gwamnatin tarayya, ta ce, za ta myar da harkokin Biza zuwa kafar Internet watau e-Visa daga ranar 1 ga watan Mayu.
Ministan harkokin cikin gida na kasar nan Tunji Ojo da takwaransa na bunkasa harkokin sufurin jiragen sama Festus Keyamo, ne suka bayyana hakan jiya laraba a birnin tarayya Abuja yayin taron dabbaka sabon tsarin a ayyukan hukumar lura da shige da fice ta kasa.
Sabuwar fasahar dai za ta bai wa masu shigowa kasar nan damar neman Biza ta Internet ba sai sun je ofishin jakadanci ba, inda hakan zai saukaka wa matafiya.
Haka kuma sun kara da cewa, a wannan sabon tsaro masu bukatar Biza za su cike dukkan bayanai ne tare da biyan kudin neman Bizar inda kuma bayan cika ka’idoji za a tura musu da Bizar ta sakon Email, kamar yadda ake yi a wasu manyan kasashen duniya.
You must be logged in to post a comment Login