Labarai
NAKSS ta buƙaci shugaba Tinubu ya cika wa ASUU alƙawura don daƙile tsundumar ta yajin aiki

Ƙungiyar ɗalibai ƴan asalin jihar Kano NAKSS shiyyar jam’iar Northwest da ke nan Kano, ta buƙaci gwamnatin tarayya da majalisun dokokin tarayya da dukkan masu ruwa da tsaki a fannin ilimi da su magance matsalolin ƙungiyar malaman jami’o’i ta ƙasa ASUU domin kauce wa tsundumarta yajin aikin sai Baba ta gani da ta ke shirin yi.
Shugaban ƙungiyar Ambasada Khalid Hassan Hudu, ne ya buƙaci hakan yayin ganawarsa da manema labarai da yammacin yau Alhamis a Kano.
Ya bayyana cewa, babu abinda yajin aikin ƙungiyar ta ASUU ke janyo wa ɗalibai ƴaƴan talakawa sai koma baya da kuma tsaiko a karatunsu.
“Mu ƴaƴan talakawa ne, iyayenmu ba su da kuɗin da za su kaimu ƙasashen waje karatu, haka kuma ba su da kuɗin da za su ɗauki nauyin karatunmu a jamio’in kuɗi da ke Najeriya, don haka muke roƙon da a taimaka mana a cika wa ASUU alƙawura ko ma samu damar yin karatun mu,” in ji Ambasada Khalid Hassan Hudu
Haka kuma, ya ƙara da cewa, “A muna kira da roƙo ga Shugaban majalisar Dattawa Sanata Godswill Akpabio da mataimakinsa Sanata Barau I Jibrin da shugaban majalisar wakilai Tajuddeen Abbas da mataimakinsa, da su taimaka su sanya baki game da wannan matsala da ke tsakanin ƙungiyar ASUU da gwamnatin tarayya don kawo ƙarshenta.”
Mudassir Adamu Musa, ɗalibi ne a sashen nazarin kimiyyar siyasa a jami’ar Bayero da ke nan Kano, ya jaddada roƙon ga shugaba Tinubu kan magance matsalolin gaza cika alkawuran da gwamnatin tarayya ta yi wa ASUU, inda ya ce, cika alkawarin zai ceci ɗalibai da dama daga samun tangarɗa a karatunsu.
Wannan roƙon na ƙungiyar ɗalibai ƴan asalin jihar Kano NAKSS na zuwa ne yayin da ya rage sa’o’i kaɗan wa’adin tsunduma yajin aikin da ƙungiyar ta bai wa gwamnatin tarayya ya cika.
You must be logged in to post a comment Login