Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kaduna

Za a yi jana’izar tsohon gwamnan Kaduna bayan sallar la’asar

Published

on

Iyalan marigayi Alhaji Abdulƙadir Balarabe Musa tsohon gwamnan tsohuwar jihar Kaduna sun ce za ayi jana’izar marigayin da karfe 4 na yamma bayan sallar la’asar.

Za ayi jana’izar a masallacin jumu’a na Sultan Bello da ke Kaduna.

Ɗaya daga cikin ƴaƴan marigayin Hajiya Zulai Balarabe Musa ce ta bayyana hakan ga Freedom Radio.

Hajiya Zulai ta ce, Sheikh Dr. Ahmad Gumi ne zai yiwa marigayin Sallah.

Marigayi Balarabe Musa ya rasu ne da safiyar Laraba a birnin Kaduna bayan ya sha fama da jinya.

Ya rasu ya bar ƴaƴa takwas da mace guda.

Muna addu’ar Allah ya jiƙansa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!