Labarai
Nan bada dadewa ba zamu kawo karshen talauci a Nijeriya: Tinubu
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya ce nan bada jimawa ba al’ummar kasar nan za su fita daga matsin rayuwar da suke ciki a yanzu.
Tinubu ya kuma ce, al’ummar Najeriya suna da kwazo wajen neman na kan su, a domin haka babu wani dalili da zai sa su ci gaba da zama a cikin Talauci.
Shugaban kasar ya bayyana hakan ne yayin da ya karbi bakuncin tawagar wasu dattawan kasar nan a fadar Villa dake Abuja.
Shugaban Tinubu ya tabbatar da cewa ‘yana sane da irin wahalar da al’ummar kasar nan ke ciki, amma yana da yakinin cewa nan bada dadewa ba za su magance matsalar.
Rahoton: Abubakar Tijjani Rabi’u
You must be logged in to post a comment Login