Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Magoya bayan jam’iyyar NNPP sun yi bikin taya Abba murna a Cross Rivers

Published

on

 

Daruruwan magoya bayan jam’iyyar NNPP da ke zaune a Unguwar Hausawa ta Jihar Cross Rivers sun yi murnar nasarar da Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya samu a Kotun Koli.

 

A Juma’ar da ta gabata ce dai Kotun Koli ta tabbatar da nasarar Gwamna Abba Kabir Yusuf a matsayi halastaccen Gwamnan Kano bayan Kotun Sauraron Kararrakin Zabe da Kotun Daukaka Kara sun haramta masa kujerar.

 

Dalilin haka ne magoya bayan jam’iyyar NNPP a Kalaba, babban birnin Kuros Riba, suka hau tituna suna bayyana farin cikinsu tare da raba wa juna kayan tanɗe-tanɗe da maƙwalashe.

 

Alhaji Danjuma Mohammed, Shugaban jam’iyyar NNPP bangaren ’yan Arewa yana cewa, nasarar da Abba Gida-Gida ya samu a shari’ar ta buɗe wani sabon babi na yafiya a siyasar Kano da kasa baki daya.

 

“Kotu ta yi adalci a wajen yanke humuncin sannan ina kira ga ’yan adawa da su zo a tafi tare domin yi wa jiha aiki da kuma ciyar da ita gaba.”

 

Ya ci gaba da cewa “Hakika Kotu ta yi adalci wajen gudanar da aikinta domin kafin yanzu har wasu daga cikin ’yan kasa sun fara dawowa daga rakiyar kotunan suna zargin ko sun fara zama ’yan amshin Shata,” inji shi.

 

  1. Haka kuma, ya shawarci Kanawa da su marawa Gwamnan baya wajen yi wa jama’a aiki, yana mai tunatar da Gwamnan ya mayar da hankali wajen inganta harkokin ilmi da kiwon lafiya musamman idan an yi la’akari da yadda wasu asibitoci da makarantu suka lalace.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!