Labarai
NAPTIP ta ceto yaran da aka sace daga arewaci zuwa kudancin Najeriya

Hukumar da ke yaƙi da safarar mutane a Najeriya, NAPTIP, ta ce ta ceto wasu yara takwas da ake zargin an sace su ne daga wasu jihohin arewacin ƙasar ciki har da jihar Kano.
Kakakin hukumar, Vincent Adekoye, ya ce an gano yaran ne a wani gidan marayu da ya yi suna a garin Asaba da ke jihar Delta a kudancin ƙasar.
Hukumar farin kaya ta DSS da jami’an ƴansanda da na civil defence ne suka ceto yaran a yayin wani samame da suka kai a gidan marayun.
Ƙawancen jamu’am tsaron sun kai samamen ne bayan ƙorafe-ƙorafen da iyayen yara suka kai na cewa ƴaƴansu sun ɓata a jihar Kano da wasu maƙwabtan jihohi.
You must be logged in to post a comment Login