Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

NARD ta zargi NMA da sanya son zuciya a lamarin ta

Published

on

Kungiyar likitoci masu neman kwarewa ta kasa NARD ta zargi kungiyar likitoci ta NMA da sanya son zuciya a cikin lamuranta, tare da ƙin fadawa gwamnatin tarayya gaskiya.

Mataimakin shugaban kungiyar Adejo Arome ne ya bayyana hakan a zantawar sa da jaridar Punch a Talatar nan.

Ya ce, shugabannin kungiyar NMA sun gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari kan wasu abubuwa da suka shafe su, inda daga baya suka bukaci kungiyar NARD ta janye yajin aikin da ta ke yi.

Tuni dai kungiyar NARD ke jaddada aniyar ta na ci gaba da yajin aiki har sai lokacin da gwamnatin ta biya musu bukatun su, kamar yadda shugaban kungiyar Uyilawa Okhuaihesuyi ke bayyanawa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!