Labarai
Nasiru El-Rufa’I ya jibge jami’an tsaro a filin jirgin saman Kaduna
Gwamanatin jihar Kaduna ta jibge jami’an tsaro a titin filin tashi da saukar jiragen sama na Jihar da nufin tabbatar da tsaro a jihar baki daya.
Wannan na zuwa ne bayan kammala tattaunawa tsakanin gwamnatin jihar Kaduna da jam’ian rundunonin tsaron kasar nan da jami’an hukumar lura da jiragen sama ta kasa da kuma shugabannin gargajiya, a kauyen Kutungare, dake yankin karamar hukumar Igabi.
A jawabin sa lokacin taron tattaunawar gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa’I, wanda Kwamishinan tsaro da kuma lura da harkokin cikin gida Samuel Aruwan ya wakilta, ya bukaci hakimai da dagatai da su bada hadin kai domin tabbatar da tsaro a lokacin karbar ta’aziyar marigayi sarkin zazzau.
Baya da Filin tashi da sauka, sauran wuraren da aka bada umarnin jibge jami’an tsaron sun hadar da Hanyar Birnin-Gwari da hanyar Kwalejin Horon jami’an soji da barakin Sojin Sama da wasu Unguwanni a jihar ta Kaduna.
You must be logged in to post a comment Login