Connect with us

Labarai

NBC ta dakatar da gidan talabijin na Channels sakamakon hira da kungiyar IPOB

Published

on

Hukumar kula da kafafen yada labarai ta radio da talabijin ta kasa (NBC) ta dakatar da tashar talabijin ta Channels sakamakon hira da ta yi da ‘yan kungiyar IPOB da ke rajin kafa ‘yan tacciyar kasar Biafra.

 

Haka zalika hukumar ta NBC ta kuma ci tarar gidan talabijin na Channels naira miliyan biyar sakamakon karya ka’idojin hukumar.

 

A cikin wata wasika da mai rikon mukamin shugaban hukumar ta NBC farfesa Armstrong Idachaba ya sanyawa hannu, ta ce, gidan talabijin na Channels ta cikin wani shiri da ya gabatar a jiya lahadi, ya tattauna da shugaban haramtacciyar kungiyar IPOB wanda kuma ya furta kalaman neman ballewa daga Najeriya.

 

A cewar NBC yin hakan ya sabawa dokokinta saboda haka ta dakatar da gidan talabijin na Channels tare da cin tararsa naira miliyan biyar.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!